Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina

Rundunar yan sandan Katsina ta halaka wani kasurgumin dan fashi a yayin wani fafatawa da suka yi a babban titin Bakori zuwa Kabomo a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa jami’an yan sanda a Bakori sun kai agaji ne a inda yan fashi suka tare hanya cikin dare, a nan ne suka halaka dan ta’addan.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya bayyana cewa: “da misalin karfe 8:30 na dare, wasu yan bindiga sun tare hanyar Bakori, sai dai mun yi nasarar dakile harinsu, sannan mun kashe daya daga cikinsu.

Gambo ya kara da cewa sauran yan ta’addan sun tsere, an kuma samu bindiga kirar hannu a wajen wanda aka halaka din.

Ya kuma ce tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano mafakar ragowar yan fashin.

A wani labari na daban, an ruwaito cewa wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wata mata mai juna biyu a Kaduna a ranar Talata a unguwar Rigachikun.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ƴan bindigan sun sace matar ne tare da mijinta daga gidansu.

Majiyar ta ce wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kashe matar yayin da suke musayar wuta da jami'an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN