Fusatattun matasa sun kashe wasu samari 2 da duka suka banka wa gawakinsu wuta


Fusatattun matasa sun yi wa wasu da ake zargin yan yan fashi da makami ne mugun duka har suka mutu, daga bisani aka banka wa gawarsu wuta a garin Benin na jihar Edo.

Lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Talata 3 ga watan Nuwamba, kusa da kasuwar Okah da ke hanyar Ighodefeyi a kan hanyar Sokponba.


An zargi matasan guda biyu da yi wa mata masu zuwa kasuwa da sassafe fashi, tare da jama'a da ke zuwa wajen aiki.

Fusatattun matasa sun yi amfani da duk makami da za su iya amfani da shi wajen afka wa yan fashin.

Bayanai sun ce bayan tarzomar EndSars da ya yi sanadin kone ofisoshin yansanda guda uku da ke . St Saviour, Ugbegun da Idogb. Yanzu haka babu jami'an tsaro a wannan yankin, lamari da ya sa bata gari ke ta cin karensu ba babbaka.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN