Za a samar da kasuwar wiwi mafi girma a Duniya


Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dattawa a Mexico, ta amince da wata doka da ake sa ran za ta bayar da dama domin samar da kasuwar sayar da wiwi mafi girma a duniya.

Idan Majalisar Wakilan ƙasar ta bayar da goyon baya kan hakan, haka kuma idan ta amince da shan wiwi domin nishaɗi, za a rinƙa amfani da tabar wiwin wurin binciken kimiyya da kuma haɗa magunguna da kuma sarrafa tabar a kamfanoni.

Wannan kudurin na zuwa ne a daidai lokacin da Mexico ke ƙoƙarin yaƙar manyan dillalan miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Source: alummata


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN