Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar ranar Asabar sun ce Najeriya ta samu komaɗar tattalin arziƙi da kaso 3.62% a third quarter of 2020, a cewar jaridar Intanet, TheCable.
Wannan shi ne karewar Ma’aunin Tattalin Arziƙi, GDP na biyu tun karewar tattalin arziƙi ta 2016. Jimillar haɓakar GDP a watanni taran farko na 2020 ya tsaya a -2.48 cikin ɗari.
Rabon da Najeriya ta samu irin wannan karyewar GDP tun a 1987, lokacin da GDPn ya yi ƙasa da kaso 10.8 cikin ɗari.
Alƙaluman da Bankin Duniya da NBS suka fitar, waɗanda jaridar TheCable ta bibiya sun ce wannan shi ne komaɗar tattalin arziƙi ta biyu da Najeriya ta samu a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na farar hula— kuma ta huɗu a matsayin Shugaban Mulkin Soja.
Source:: labarai24
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari