Za a kashe wani makiyayi bayan Kotu ta same shi da laifin kashe dansa saboda N1m


Wata babban Kotu a Yola na jihar Adamawa ,ta yanke ma wani Makiyayi hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin kashe dansa na cikinsa mai shekara biyar saboda Naira Miliyan daya.

Alkalin Kotun Jastis Fatima Ahmed Tafida ta yanke wa Bappa hukuncin kisan ne domin ya sa icen da yake kiwo da shi ya buge dansa a kai, daga bisani ya sare kansa da adda.

Tsohon dan Fursuna Bappa mai shekara 24 a Duniya, ya lallaba yaronsa ne mai suna Buba zuwa cikin daji ranar 13 ga watan Yuli 2013 a kauyen Ganji da ke karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa, kuma ya sare kansa.

Sai dai Kakan yaron mai suna Alhaji Guza, ya nemi sanin bayanin inda dansa yake, amma mahaifinsa Bappa ya ce ya baro shi a daji kuma zai dawo.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari