Yaro Ɗan shekara 14 ya kashe duka ahalinsu bayan gano mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce


Wani matashin yaro ya harbe iyayensa da ƴan'uwansa ƙanana guda 3 har lahira bayan ya gano cewa wadda ya ɗauka a mahaifiyarsa kishiyar uwarsa ce da ta rike shi. Sai dai kuma duk da ya kashe 'yan uwansa yaron ko kaɗan bai nuna nadamarsa ba.

A yanzu haka yaron mai suna Masom Sisk, ya na da shekaru 15 a duniya. Wanda ake zargi da kisan kiyashin kwata-kwata bai nuna damuwa a kan irin ɓarnar da ya aikata ba. Ana zarginsa da laifin ne a kotun yara ta Limestone County,Alabama,a watan Satumbar 2019.

Shugaban sashen wa'adin gyara hali na ɓangaren yara a Limestone County,Jami'i Tara Pressnell yace;. "Mason bai nuna wata alamar damuwa ko nadama a bisa laifin da ake tuhumarsa na kashe iyalansa ba. Lokacin da ake tsare dashi bai taɓa hira ko magana akan iyalinsa ba ko kaɗan."

Matashin bai nuna kaico da nadamar aikita laifin da yayi ba. Ana tuhumarsa ne yi a matsayin baligi da laifin kashe rayuka biyar murus har lahira. An ce ya yi harbe-harben ne jim kaɗan bayan ya gano cewar Mary Sisk, ƴar shekara 35, ba ita ce uwar data haife shi ba, duk da har yanzu masu bincike basu tabbatar da batun ba.

Ana zargin Sisk da kashe mahaifinsa John Sisk,mai shekara 38, Kishiyar babarsa Mary Sisk, mai shekaru 35, ɗan uwansa, Grayson, mai shekaru 6, ƴar uwarsa; Aurora, mai shekaru biyar, da kuma ɗan uwansa jinjiri ɗan wata shida mai suna Colson a gidansu dake Elkmont.

Alƙalin kotun yara, mai shari'a Mathew Huggins ya ce babu wani dalili da zai nuna Sisk ya na da taɓin hankali ko matsalar ƙwaƙwalwa lamarin mai rikitarwa gami da ɗimautarwa , a saboda haka ne kotu ta bayar da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan yarin Limestone County.

Rahotanni sun nuna yadda Sisk ya ke kammala aikinsa na makaranta da mu'ammala tare da sauran yara a wajen ajiye yara masu laifi na jihar Tennessee.Da farko an yi zaton Sisk zai ɗorawa wani zargin,sai dai ya amsa da bakinsa cewa shine ya aikata ta'asar lokacin da aka tambaye shi a gaban kotu.

Kishiyar mahaifiyarsa, Mary, malama ce da ɗalibai suke ƙaunarta a makarantar Mountain Gap tare da mahaifin Sisk, mai suna John, ƙwarren mai aikin kwalliya da zanen fuska wanda ya kasance fitacce kuma mutum mai son zaman lafiya, barkwanci da raha tare da abokansa da kuma abokan aikinsa.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN