Yadda za ki gane ko da gaske saurayinki yana sonki da aure ne ko akasin haka


Ko kina tababa cewa wane irin soyayya saurayin ki yake maki?  Ko soyayyar shi ta gaske ne ko yana son ki ne kawai don wata manufa ko biyan bukata?. Duba wadannan ababe a kasa da ya kamata ki lura.

1. Idan yana yawan zance surar jikin ki

Duk da yake tabbas mata na da surar halitta mai kyau, idan a ko da yaushe saurayinki zancensa shi ne kina da kyau, amma baya kawo wasu kyawawan ababe game da ke, kamar halinki, addini, mu'amalarki ko ababe makamantan haka.

2. Idan yana yawan son ya taba jikinki

Idan saurayinki yana yawan son ya taba jikinki, ko wani sashe na jikinki, wani sa ilin wasu samari har  da kokarin rungumar budurwarsu. Sai ki lura cewa akwai abin da yake so a jikinki amma ba wai ke ce yake so ba. Kuma idan kika bari ya samu, lallai zai gudu kuma  ba mamaki za ki yi nadama.

3 Baya son ya yi maganar aure

Matukar saurayi yana hulda da ke, tun farko ki tantance wane irin hulda kuke yi. Idan ya nuna ai yana kaunarki ne da aure, sai ki lura ko yana yawan zance auren idan kuna tare. Idan ba haka ba wata kila ba da gaske yake yi ba, sakamakon haka sai ki nemi tantance gaskiyar lamari kafin tafiya ta yi nisa.

Nazari daga Isyaku Garba Zuru


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN