Yadda rikicin Rahama Sadau ya janyo rikicin cikin gida da rabewar kai a Kannywood


Kamar yadda rahotonni suka kammala, jaruma Hafsat Shehu wacce tayi aure babu jimawa kuma auren ya mutu da kuma jaruma Mansura Isah sun yi musayar yawu.

Bayan caccakar juna da suka yi, Mansura Isah ta yi gaggawar goge tsokacin da tayi, inda kafafen sada zumunta suka dauki zafi, Daily Trust ta wallafa.

Mansurah tayi amfani da shafinta na Instagram inda tace da bata so yin magana ba, amma kowa yana zunubi. Kuma kowa yana da kashi a gindinsa.

Ya kamata a dakata da caccakar Sadau haka, duk masu caccakarta sanye da hijabai duk na munafurci ne, suna yaudarar mutane. Su ji tsoron Allah, kuma su duba abubuwan da suka aikata a baya.

Bayan ganin wannan wallafar ta Mansurah, Hafsat Shehu tayi tsokaci a kasan wallafar, inda tace "Mun san matan aure masu bin maza, kuma kowa yana zunubi, kowa yana da nashi guntun kashin."

Tsohuwar jaruma Fati Slow kuma ta yi bidiyo, inda tace kada a bari su fara sakin bama-bamai a kan matan Yarabawa. Matsawar Mansura ta sake magana, za su "tona mata asiri."

Jaruma Rashida mai sa'a ta ce wannan sa-in-sa da 'yan Kannywood suke yi alama ce da take nuna cewa kan duk jaruman Kannywood a rabe yake.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN