Wata Kotun Majistare a birnin Abuja, ranar 11 ga watan Nowamba, ta bayar da belin Paul Akinwumi, Davo Chom, Abdulsalam Suberu, Kabiru Gasali, Yaziru Bashiru da wataa yar Jarida da take daukan labarai a lokacin zanga zangar EndSars.
The Cable ta labarta cewa an garkame masu zanga zangan ne a Kurkuku bayan Alkalin Kotun ya ki amincewa da neman belin wadanda aka yi kara a gaban Kotun da Lauyansu Tope Akinyode ya gabatar.
Sai dai a zaman Kotun na ranar Laraba, Alkalin Kotun Abdulrazak Eneye, ya bayar da belinsu a kan Naira dubu hamsin kowannensu tare da wadanda zai tsaya wa kowannensu.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari