Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola


Wata kotun majistare na Osun da ke zama a Oshogbo a ranar Laraba, ta garkame wasu mata biyu a gidan gyara hali na Ilesha kan zargin yunkurin kashe Gwamna Adegboyega Oyetola.

Matan da aka bayyana a matsayin Suliat Tajudeen mai shekaru 20 da Ayomide Abdulazeez mai shekaru 20, ana tuhumarsu da hada kai wajen yunkurin kisa, barna da kuma sata. Dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Idoko, ya sanar da kotu cewa Suliyat, Ayomide da wasu a ranar 17 ga watan Oktoban 2020, da misalin karfe 4:30 na rana, sun hada kai a yunkurin kashe Oyetola ta hanyar bude masa wutan harbi da jefarsa da duwatsu.

Sun fasa shagon Justrite sannan suka sace na’urorin Laptop, wayoyin hannu da sauran kayayyaki da suka kai kimanin naira miliyan 3,568,000 mallakar Ashiru Ibrahim Olayemi. Sai dai wadanda ake zargin basu amsa tuhume-tuhume biyar da yan sanda ke masu ba. 

Lauyansu, Nurudeen Kareem, ya nemi a bayar da belin wadanda yake karewa inda ya ba kotun tabbacin samar da jingina abun dogaro.

Sai dai, mai kara ya nuna adawa da bukatar wanda ake kara, cewa idan aka basu beli za su gudu, saboda wadanda ake karar sun san cewa na da hujja a kansu. Alkalin kotun, Dr Ayilara ya tsare wadanda ake zargin a gidan gyara hali na Ilesha sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2020, don zartar da hukunci kan bukatar belin.Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN