Yanzu yanzu: IGP Adamu ya maka tsohon gwamnan Imo kotu saboda yada labaran karya


A ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedioha Ohakim, a gaban wata babbar kotu a birnin tarayya kan zargin bayar da bayanan karya.

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ne ya gurfanar da Ohakim a kan wasu tuhume-tuhume uku a gaban kotun da ke Abuja. Sai dai kuma, mai alkalin da ke jagorantar shari’a, Justis Samira Bature, ta bayar da belin tsohon gwamnan kan naira miliyan 10 bayan ya ki amsa laifinsa, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

An bayar da belin nasa ne a matsayin amsa ga ikirarin lauyan Ohakim, K.C.O Njemanze, wanda ya yi ikirarin cewa tuhume-tuhumen da ake yiwa wanda yake karewa na iya samun beli, matsayar da lauyan mai kara, Stanley Nwodo ya yi adawa da shi.

A wani labarin, wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, Zone 6, ta gurfanar da mamba a majalisar wakilai, Mista Victor Mela, bisa zarginsa da bayar da bayanan karya ga hukumar zabe ta kasa (INEC) tare da yin rantsuwa a kan cewa gaskiya ne.

Hukumar 'yan sandan birnin tarayya (FCT), Abuja, ce ta gurfanar da Mista Mela bayan zarginsa da rattaba hannu, a matsayin rantsuwa, a kan bayanana karya da ya bayar yayin cike fom din hukumar INEC mai lamba CF001 gabanin zaben 2019

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari