Yansanda sun yi ram da wata mata mai bawa ƴanfashi, ɓarayi da masu laifi mafaka


Ƴan sandan jihar Bauchi sun kama wata mata da ake zargi da bawa masu muggan laifuka mafaka sakamakon kama ɓarayi biyu da ƴan fashi a gidanta.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, DSP Mohammed Ahmed Wakili, shine ya bayyana hakan ranar a Alhamis.

Ya ce jami'an rundunar, bayan samun bayanan sirri, sun kama wata Sadiya Mohammed Yaro wacce aka fi sani da Sadiya Ƙaura, ƴar shekara 28, a unguwar ƙofar Dumi ta garin Bauchi.

Acewarsa, matar ta bawa masu laifi mafaka a gidanta dake ƙofar Ɗumi jim kaɗan bayan sun kai hari ofishin Komiti a garin Bauchi.

An ji matar ta naɗi muryarta tana kirari da yabon ƴan daban, tana mai goyon ɓayansu.


Wakili ya ce ƴansanda sun kama masu laifi biyu masu suna; Yakubu Hussaini wanda aka fi sani da Abba Laba, mai shekaru 20.

Sai kuma Bashir Ahmad wanda aka fi sani da Bashoo, mai shekaru 23, dukkansu daga ƙofar Ɗumi, kuma suna cikin sanannu ƴan daban da suka addabi jihohin Bauchi, Gombe, Plateau da Kaduna.

Ya ce ƴan ta'addan sun tsere daga hannun hukuma a shekar 2019.

Ya kara da cewa suna daga cikin waɗanda suka kai harin Ofishin kwamiti a unguwannin Zango da Ƙofar Ɗumi a jihar Bauchi.

Za'a shigar da laifunsu sannan a gurfanar da su a gaban kuliya su girbi abin da shuka, a cewarsa.

Legit.ng Hausa ta rawaito Dakta Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, na yin kira ga 'yan Najeriya da su mika al'amuransu ga Allah.

A cewar gwamna Okowa, alhakin jama'a ne su ririta rayuwarsu saboda al'amura sun rincabe a Nigeria.: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN