'Yan jarida, 'yan sanda, sojoji ba za su kaɗa ƙuri'a ba a ranar zaɓe a Ghana


Hukumar zaɓen Ghana ta ce 'yan sanda da sojoji da 'yan jarida da direbobin motar ɗaukar marsa lafiya ba za su jefa ƙuri'a ba a zaɓen ranar 7 ga watan Disamba mai zuwa.

Hukumar Ghana Electoral Commission (GEC) ta ce waɗannan rukunin mutanen da ta lissafa na cikin masu kaɗa ƙuri'a na musamman da za su yi zaɓen tun 1 ga Disamba.

Tuni GEC ta wallafa sunayen waɗanda za su jefa ƙuri'ar a rana ta musamman ga mutanen da ke aiki na musamman, waɗanda kaɗa ƙuri'ar ka iya shafar aikinsu a ranar zaɓe.

Mutanen sun haɗa da 'yan sanda da sojoji da masu tuƙa motocin ɗaukar marasa lafiya da 'yan jarida da sauransu.

Sai dai hukumar ta gargaɗi waɗanda suka yi rajistar zaɓe na musamman cewa idan suka gaza kaɗa ƙuri'a ranar 1 ga wata to ba za su yi zaɓen ba ranar 7.

"Wajibi ne masu zaɓen su tabbatar cewa sun bi matakan da suka dace domin tantance bayanansu saboda gudun kar a haramta musu kaɗa ƙuri'a tun da GEC ba za ta bari su yi zaɓe ba ranar 7 ga wata," in ji hukumar. 

Source: BBC


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN