• Labaran yau


  Yadda aka farmaki masallata a Masallacin Juma'a a Dutsin dosa, Danko-Wasagu jihar Kebbi


  Ana zargin cewa wasu mutane sun afka wa jama'a da ke Sallah a cikin wani Masallacin Juma'a da harbi a kusa da Dutsin dosa, sakamakon haka wani mutum mai suna Dahiru ya rasa ransa. An raunata mutum uku, kazalika aka dauke wa mamacin wayarshi ta salula ta kimanin dubu hamsin, da kudinsa kusan Naira dubu sittin, da babur Boza, a lokacin hargitsi da kutsawar mutanen ya haifar bayan sun yi ta harbe harbe ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Danko-Wasagu da ke kudaancin jihar Kebbi a tarayyar Najeriya.

  Bayanai sun tabbatar cewa wanda aka kashe mai suna Malam Dahiru, yaya ne ga wanda aka raunata ta hanyar karya masa hannu a lokacin farmakin.

  Wannan yana zuwa ne bayan an yi zargin cewa barayi sun shiga garin Dan kolo kwanaki uku da suka gabata, suka kori shanu kusan Nagge dari biyar a kauyukan Fulani. Bayanai sun ce babu wanda ya tare barayin. Kazalika an yi zargin cewa barayin sun farfasa shaguna a garin Dan kolo, suka kwashi kayaki da dama.

  Majiyarmu ta yi zargin cewa ana kyautata zaton cewa barayin sun shige jihar Zamfara da shanayen. Wata majiya ta ce " Da suka kori shanun, ana kyautata zaton cewa sun bi ta Kotonkoro, suka bi ta Mai laka, daga nan suka wuce suka shiga Zamfara dasu".

  Kudancin jihar Kebbi da ta yi iyaka da jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, musamman yankin kananan hukumomin Danko-Wasagu, Sakaba, Fakai da Zuru sakamakon ayyukan yan bindiga da barayin shanu.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka farmaki masallata a Masallacin Juma'a a Dutsin dosa, Danko-Wasagu jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama