Wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar wanda aka fi sani da suna Iro, ya kashe kanshi ta hanyar rataye kanshi a cikin shagonsa har ya mutu a unguwar Zoo da ke Kano.
Today.ng ta labarta cewa Iro ya halarci Sallar La'asar tare da sauran jama'a. Amma bayan kammala Salla sai ya bi ta shagon abokinsa ya karbi igiya ya wuce shago.
Isarsa shago ke da wuya sai ya aiki dansa ya sayo masa abinci, kazalika ya aiki ragowar daya yaron mai koyon aiki a shagonsa. Bayan sun tafi ne sai ya rufe kanshi a cikin shago ya rataye kanshi har ya mutu.
Marigayi Iro yana sana'ar sayar da baturi da tayar mota ne kafin mutuwarsa.
Bayan yaronsa ya kula cewa an dauki lokaci mai tsawo mahaifinsa bai fito daga cikin shago ba, sai ya sanar da makwabta, su kuma suka kira yansanda, aka balle kofar shago aka gan gawarsa tana lilo a fankan sama a cikin shagon.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari