Muni da hadarin shigar tsiraici ga mata


Daga Imam Murtada Muhammad Gusau
(Abu Mus’ab)
Masallacin Juma’a na Nagazi,
Okene Jihar Kogi

Huduba ta Farko:

Lallai dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai renon halittu, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu.

Lallai wanda Allah Ya shiryar babu bata a gare shi, kuma wanda Ya batar babu shiriya a gare shi. Ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa ne. “Ya ku wadanda suka yi imani! Kubi Allah da takawa, a kan hakkin bin Sa da takawa, kada ku yarda ku mutu face kuna masu sallamawa (wato Musulmi).” (Ali-Imran:102). “Ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah Wanda Ya halitta ku daga rai daya (Adamu), kuma Ya halitta daga gare shi matarsa (Hauwa’u) kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku ji tsoron Allah, Wanda kuke rokon juna da sunanSa, kuma da zumunta. Lallai Allah Ya kasance mai tsaro a kanku.” (Nisa’i:1).

“Ya ku wadanda suka yi Imani! Ku ji tsoron Allah, kuma ku fadi magana madaidaiciya. Sai Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa, to, lallai ya rabauta, rabo mai girma. (Ahzab:70-71).

Bayan haka, lallai ku sani mafi gaskiyar zance, shi ne zancen Allah (SWT) kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammad (SAW), kuma mafi sharrin al’amura, su ne wadanda aka kirkira (cikin addini), kuma dukan kirkirarrun al’amura bidi’a ne, kuma dukan bidi’a bata ce, kuma dukan bata makomarta wuta. Ina rokon Allah Ya kare mu daga wuta, amin.

Ya ku Musulmi masu girma! Lallai ina yi muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah Mai girma da daukaka, domin tsoron Allah shi ne tushen dukan alherin duniya da Lahira. Kuma shi ne ginshikin rabauta a nan duniya da Lahira.

A yau Hudubarmu za ta yi tsokaci ne a kan irin mummunar shigar tsiraici da ’yan uwanmu mata suke yi. Wannan maudu’i na yau kamar amsa ce game da tambaya da rokon da wata ’yar uwa daga Jami’ar Legas ta yi cewa don Allah tana rokon a yi Huduba a kan wannan maudu’i. Ina rokon Allah Ya shiryar da mu baki daya, amin.

Ya ku Musulmi! Lallai yana daga cikin Abubuwan da makiyanmu suka yake mu da shi kuma suka ci nasara a kanmu a wannan zamani, shi ne kwararowar wasu irin tufafi, da wasu nau’ukan dinke-dinke marasa kan gado da suka yadu cikin al’ummar Musulmi.

Wadannan tufafi ba sa suturce al’aura saboda gajartarsu, kuma wasu shara –shara ne ko masu matse jiki. Irin wadannan tufafi a Musulunci harum ne mace ta sanya su, koda a gaban mata ’yan uwanta ko gaban muharramanta, bare kuma wasu wadanda ba su ba.

Lallai mu sani yana daga alamomin kusantowar Alkiyama, bayyanar shigar tsiraici, ta hanyar sanya matsatstsun tufafi masu bayyana surar jikin mace, ko tufafi masu shara-shara, ko masu wani irin tsagu, ko wani irin tufafi ko dinki da zai kasance kirjin mace da bayanta duk a fili ko cinyoyinta ko kafafuwanta. Irin wadannan mata a zahiri za ka ga sun sanya tufafi amma a hakikanin gaskiya tsirara suke.

Hakika Annabi (SAW) ya ba mu labari game da bayyanar wadannan nau’ukan tufafi na mata a karshen zamani, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (RA) ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Akwai nau’i biyu na ’yan wuta ban gansu a zamanina ba. Sai Annabi (SAW) ya ce; na farko, wasu mutane ne tare da su akwai bulala ko dorina kamar jelar shanu, suna dukan mutane da ita: sannan na biyu;

mata ne, sun sanyan tufafi amma tsirara suke, karkatattu masu karkatarwa, kawunansu kamar tozon rakumi karkatacce, ba za su shiga Aljanna ba, kai ba ma za su ji kanshinta ba, alhali kuwa ana jiyo kanshinta tun daga tafiyar nisan kaza da kaza.” Muslim ne ya ruwaito kuma Sheikh Muhammad Nasiruddin al-Albaniy ya igannta shi a cikin Sahihul Jami’u, Hadisi na 2,128.

Ya ku Musulmi! Lallai idan muka natsu da kyau, muka fahimci wannan Hadisi, za mu ga irin muni da hadarin da matan wannan al’umma suke ciki, saboda koyi da kafirai a wurin sanya tufafi. An wayi gari a yau, idan ka ga wata Musulma ba ka iya bambance ta da wadda ba Musulma ba. Wani lokaci sai an kira sunanta sannan za ka ce ashe wannan Musulma ce? Ya ku al’umma! Lallai ya zama wajibi mu ji tsoron Allah a kan matanmu da ’ya’yanmu da kannenmu da yayyenmu da duk matan wannan al’umma. Mu sani mu abin tambaya ne game da wadannan bayin Allah.

Yau an wayi gari sanadiyyar irin wannan shigar banza ta nuna tsiraici, zinace-zinace sun yi yawa a cikin al’umma, a yau ko’ina a duniya duk inda ka shiga za ka ji ana surutai da maganganu a kan fyade, kuma ba komai ke jawo wannan ba illa kin bin umarnin da Allah Ya yi a kan sanya Hijabi. Allah (SWT) Ya fada a LittafinSa Mai girma cewa: “Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka da ’ya’yanka da matan muminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauki ga a gane su, domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jinkai?” (Ahzab:59).

Ya kai dan uwa mai sauraro! Ka sani lallai wannan aya tana mana umarnin Allah a kan yin Hijabi, ga matan Annabi (SAW) da ’ya’yansa da matan dukan muminai. Bin umarnin Allah shi zai kare su ba za a cutar da su ba (fyade). Sannan zai nuna cewa su fa Musulmi ne ba kafirai ba.

Ya Allah! Ka shiryar da mu, Ka shiryar da matan Musulmi su dawo kan hanya, su bar irin wannan mummunar shiga ta tsiraici, amin. Allah Ka gafarta mana da dukan Musulmi a duk inda suke a duniya, amin.

Huduba ta Biyu:

Hamdala da godiya ga Allah.

Bayan haka ya ku Musulmi! Lallai ya zama dole mu yi tsayin daka, mu nuna wa matan wannan al’umma, muni da tasirin irin wannan shigar tsiraici. Kuma mu nuna musu lallai Allah da ManzonSa (SAW) sun haramta wa Musulmi koyi da kafirai, domin Manzon Allah (SWA) ya ce “Wanda ya kamantu da mutane, to yana cikinsu.” Koyi da mutane alama ce ta nuna kauna a gare su; kuma Annabi (SAW) ya ce: “Mutum yana tare da wadanda yake so ranar Alkiyama.” Ya wajaba a matasayinmu na Musulmi mu kiyaye wannan.

Sannan a matsayinki na Musulma, ya kamata da an gan ki a san cewa lallai ke Musulma ce, ta hanyar shigarki kawai.

Sannan mace ta sani, ya zama wajibi ta kaurace wa duk wata shiga ta Jahiliyya, idan ya kama za ta fita saboda wata lalura, to, ta yi shiga irin ta Musulunci, domin ta kauce wa fushin Allah da sharrin miyagu.
Allah (SWT) Yana cewa: “Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kada ku yi fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta Jahiliyyar farko. Kuma ku tsai da Sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi da’a ga Allah da ManzonSa. Allah Yana nufin Ya tafiyar da kazanta daga gare ku, ya mutanen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakewa.” (Ahzab:33).

Ya ku Musulmi! Mu ji tsoron Allah mu gyara da kanmu kafin Allah Ya gyara da kanSa, domin mu tsira a nan duniya da Lahira. Ku duba makarantunmu a yau, tun daga firamare har sakandare da jami’oi’i, iyaye da malamai suna kallo ana munanan shiga na nuna tsiraici amma gyara ya gagara. Koda yake alhamdu lillahi a wasu makarantu musamman na arewa, ana kokarin gyarawa. To Allah Ya taimake mu Ya ba mu ikon gyarawa, amin.

Ya Allah! Ina rokon Ka ba mu imani na gaskiya da cikakken yaakini. Ka ba mu dauwamammiyar ni’ima da farin ciki da ba sa yankewa. Ka ba mu amincewa da abin da Ka hukunta da kwanciyar hankali bayan mutuwa, ka azurta mu da dubi zuwa ga fuskarKa mai daraja ya Allah! Ya Allah! Ka shiryar da mu da zuriyarmu, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka rufa mana asiri duniya da Lahira.

A KULA, WANNAN HUDUBAR AN YI NE MAKONNI DA SUKA GABATA. ALHAMDU LILLAH.

Source: alummata


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN