Sifetan dan sanda ya yi budurwa fyade, yana barazanar kashe kan shi idan ba a yafe masa ba

Sifetan dan sanda ya yi budurwa fyade, yana barazanar kashe kan shi idan ba a yafe masa ba


An kama wani sifetan 'yan sanda mai aiki da ofishin 'yan sanda na Agbado, jihar Legas mai suna Adelakun Amubeiya, da laifin yi wa wata dalibar jami'a, Joy (ba sunanta na asali ba) fyade, a wuraren Ipaja dake jihar Legas.

Punch Metro sun tattaro bayanai a kan yadda wanda ake zargin da yarinyar suna zaune a haraba daya ne a Abesan Estate.

Dan sandan da matarsa sun sha alwashin taimaka wa yarinyar yadda za ta samu kudi ta wayarta. A ranar 15 ga watan Nuwamba, yarinyar mai shekaru 18 taje gidan, inda ta tarar da Amubieya shi kadai

Dan sandan ya jata ta karfi da yaji har kan gadonsa, inda yayi mata fyade.

Joy ta tabbatar wa da Punch Metro cewa ta yi iyakar kokarinta don ya kyaleta, amma ya murje idonsa ya zage, har sai da ya cimma manufarsa.

Bayan mahaifin yarinyar ya samu labarin fyaden, ya samu wanda ake zargin yayi fyaden, yayi masa magana amma ya musanta.

"Cewa yayi diya ta ta yi masa kazafi. Na kaita asibiti inda suka yi mata gwaje-gwaje. Na kai kara ofishin 'yan sanda da ke Ipaja. Da 'yan sandan suka je gidansa, basu sameshi ba. Sannan an je ofishinsa amma ba a ganshi ba, sannan na kai karar su wurin masu rajin kare hakkin bil'adama.

"Bayan 'yan sanda sinyita jiranshi a ofishinsu dake Ipaja amma yaki zuwa, sai aka mayar da karar zuwa Ikeja."

"Har ranar Litinin bai bayyana ba, sai mutane da yake ta turowa su rokeni. Da na tambayeshi dalilinsa na yi wa diyata fyade, sai yace sharrin shaidan ne. Ina so ayi wa yarinyata adalci, don yanzu haka tana cikin matsanancin hali," a cewarsa.

Shugabar wata hukumar kare hakkin yara, Esther Ogwu ta shawarci iyaye da su dinga kula da yaransu. "Inaso in shawarci iyaye da su zaunar da yara su fahimtar da su matsalar shiga gidan mutane saboda akwai matsalar hakan."

Jami'in hulda da jama'a na jihar, Muyiwa Adejobi, ya yi alkawarin tsayawa tsayin-daka a kan al'amarin.

A wani labari na daban, akasin kiran da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yayi na batun karba-karba tsakanin yankunan Najeriya wurin mulki, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce karba-karba ba zai taimaki Najeriya ba, ko kuma kawo karshen matsalolin da kasar nan take fuskanta ba.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN