An tsinci gawar wata budurwa a cikin wani gwata a kauyen Aodikpi da ke kan hanyar Osumenyi/Akwuihedi a Osumenyi da ke karamar hukumar Nnewi na yamma a jihar Anambra.
Ba a gane ko wacece ba, sai dai an sami gawar an daure hannaye da kafafunta da igiya, kazalika an daure bakinta da igiya domin kada ta yi ihu.
An lura akwai alamar budurwar ta fuskanci tashin hankali da tarzoma kafin a kashe ta kamar yadda alamu suka bayyana a wuyanta.
Kakakin hukumar yansandan jihar Anambara Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda na bincike domin ganowa tare da kama wadanda suka aikata wannan aiki.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari