Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170


Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu (IPMAN) ta siffanta karin farashin Depot na man fetur daga 147.67 zuwa 155.75 ba tare da la'akarin irin halin kuncin da al'umma ke ciki ba. Farashin Depot shine farashin da ake sayarwa yan kasuwan man fetur, sannan su sanya nasu farashin kafin sayarwa yan Najeriya.

IPMAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatad da wannan karin da hukumar NNPC ta sanar. Shugaban kungiyar IPMAN, yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajudeen, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abeokuta, birnin jihar Ogun, Vanguard ta ruwaito. Ya ce kungiyar na rokon gwamnatin tarayya saboda gudun fushin jama'an kasar dake fuskantar matsalar tattalin arziki.

A cewarsa, wannan kari zai shafi kudin jigilar mai, kudin lodi, kuma gwamnati ba ta tunanin halin da yan kasuwa da al'ummar kasa ke ciki. "Saboda haka muna rokon gwamnatin tarayya ta dakatad da karin har sai an samu saukin lamura," Tajudeen yace.

"Ba tare da tunanin halin da masu ruwa da tsaki ke ciki, gwamnatin tarayya ta sanar da sabon farashin da shugabannin NNPC suka ce za'a fara yau, Juma'a, 13 ga Nuwamba, 2002." Ya bayyana cewa IPMAN za tayi ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki domin tattauna lamarin.

Mun kawo muku cewa yan Najeriya su shirya hauhawar farashin man fetur kwanan nan a fadin tarayya saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ta kara daga N147.67 zuwa N155.17, Premium Times ta ruwaito. Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai. 

A takardar da kamfanin ta saki ranar 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020. R

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN