Jihar Kwara za ta dena biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu fansho


Gwamnatin Jihar Kwara zata soke dokar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudaden fansho kamar yadda gwamnan jihar ya sanar a shafinsa na Twitter. Wannan matakin ya yi kama da wadda gwamnatin Jihar Legas ta dauka a baya bayan nan inda ta ce za ta dena biyan tsaffin gwamnonin da mataimakansu kudaden fansho.

Gwamna Abdulrazak yace jihar na bukatar kudade don inganta rayuwar al'ummar jihar, inda ya ce ya yi imanin zai fi dacewa ayi amfani da kudaden jihar wurin magance talauci da samar wa matasa ayyukan yi.

A bangarenta, gwamnatin na Legas ta ce ta dauki matakin ne don rage kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa a kansu don ta mayar da hankali kan yin ayyukan da zasu inganta rayuwar 'yan jihar.

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu a martanin da ya yi ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin na Legas karkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta dauka. Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APC zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari