Trump ya sa jirginsa mai saukar Angulu kasuwa kwana daya bayan ya sha kasa a zabe


Shugaban Amurka Donald Trump ya sa daya daga cikin Jiragensa mai saukar Angulu kasuwa domin sayarwa.

A rahotun TMZ, Trump na da  Jiragen sama masu saukar Angulu sumfurin Sikorsky S76-B guda uku, kuma ba su da alaka da Fadar Gwamnati.


An kiyasta kudin Jirgin zai kai Dala $700,000-$800,000, yayin da sabon kiran Jirgin zai kai darajar Dala Miliyan daya $1 zuwa Dala Miliyan biyu $2m.

Tun da ya zama shugaban kasa a 2017 kuma aka bashi Jirgin shugaban kasar Amurka Air-Force-One, da kuma jirgi mai saukar Angulu na shugaban kasar Amurka Marine-One, Trump bai shiga Jirginsa kirar Sikorsky S76-B ba.


Wannan labari ya bulla ne kwana daya bayan dan takaran shugabn kasar Amurka a jam'iyar Republican Donald Trump, ya sha kasa a wajen dan takarar shugabn kasa a karkashin jam'iyar Democrat Joe Biden. 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari