• Labaran yau

  An kashe Pasto da aka zarge shi da sace mazakuta a jihar Benue, an kone gidaje da Chochin sa


  An kashe Malamin Mujami'a da aka zarge shi da sace Mazakutar matasa a garin Daudu na jihar Benue.

  Hadimin Gwamnan Benue kan harkar labarai Olikita Ekani ya ce an kashe Pastor Uhembe Jacob kuma a ka bizine gawarsa a wani kabari mara zurfi.

  Yayin da ya sako hotunan Pasto Ehembe, Ekani ya ruwaito cewa  "Babban la'ana a garin Daudu"  "Wannan shi ne Pastot Uhembe Jacob wanda aka yi wa kazafin sace Mazakutar jama'a a garin Daudu"

  "Bayan sun kone duk gidajensa, Mujami'arsa, tare da duk abin da ya mallaka, daga karshe sun sace shi suka tafi da shi daji suka kashe shi a kan lamari da bai san komi ba akai, kuma suka bizine shi a kabari da babu zurfi.

  " Laifinsa kwaya daya ne kadai tilau...domin yana samun ci gaba cikin gaggawa!" inji Ekani.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe Pasto da aka zarge shi da sace mazakuta a jihar Benue, an kone gidaje da Chochin sa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama