Ta gutsure mazakutarsa bayan ya yi mata fyade


Wata mata mai suna Juaninta ’yar shekaru 24, ta gutsure mazakutar wani mutum wanda bayan ya yi mata fyade kuma ya nemi ta tsotsi gabansa.

Lamarin ya faru ne jiya Asabar a Obuasi, yankin Ashanti na kasar Ghana yayin da mutumin ya shiga dakin matashiyar da tsakar dare kamar yadda Kakakin ’Yan sandan yankin ASP Godwin Ahianyo ya bai wa manema labarai tabbaci.

Rahoton da BBC ya ruwaito ya ce mutumin mai suna Emmanuel Ankron mai shekaru 23, ya shiga dakin matashiyar wadda ta kasance daliba kuma ya nemi ta tsotsi mazakutarsa bayan ya yi mata fashi da makami wajen karbe mata dukiya.

A yayin da ta ke amsa bukatar Emmanuel ne Juaninta ta yanke shawarar gantsarawa mazakutarsa cizo da har ta kai shi ga kwanciya a gadon asibiti.

Ganin yadda jini ke tsiyaya daga gabansa ne ya santa ya tsere yayin da ita kuwa ta yi gaggawar kai kanta asibitin Anglogold Ashanti domin a duba lafiyarta.

Ana tsaka da duba lafiyarta ne a asibitin sai ga Emmanuel shi ma ya kai kansa asibitin inda cikin firgici ta gaggauta shigar da korafi kuma jami’an ’yan sanda suka yi ram da shi.

Binciken ’yan sanda ya gano gutsuren mazakutar matashin da Juaninta ta cizge da hakoronta yayin da ta ke tsotse masa gaba bayan ya yi mata fyade.

Source: Jaridar Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN