Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa


Jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Fati Slow-motion ta mayar da martani ga Mansura Isa a kan fallasar da ta yi wa yan matan Kannywood da suka caccaki Rahama Sadau kan shigar da tayi.

Fati ta gargadi Mansura a kan ta kiyaye ta don kada ta bari su yi tone-tone, idan ba haka ba sai ta kwance mata zani a kasuwa. Ta kuma shawarceta da ta je ta rungumi aurenta maimakon ganinta da ake yi a tsakiyar maza a koda yaushe.Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa:

“Budidaddiyar wasika zuwa gareki bayarabiya yar tuwo tuwo nagode Allah nake karya banida aure ai matar aure karya tafi illar akan budurwa kuma Dan ubanki ke kinsan baki da gori akaina ko ada nina bar maki miji kika aura amma wallah idan kika cigaba da Kare masu laifi zanci ubanki na nuna maki ni mara kunyar CE ta gaske ai bansan kinyi ba sai yanxu nagani kinabata suna mace mai daraja akannywood wadda tafiki nĂ saba da tarihi mai kyau arayuwa kowa yasani @hafsatshehu48 @rashidamaisaa ita uwarkice taci uwarki arashin kunya da sanin manya ita tanada bakin da zata kare kanta shrgiya yar dakan kuka yar maula yar ci da addini kina cinye kudin miskinan kiji tsoran allah ki kulada da matsalar gabanki.”

A baya mun ji cewa, tun bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau, wadanda suka kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, mutane da dama musamman 'yan fim suka yi ta yin bidiyo suna la'antarta, har da masu hawayen takaici da bakinciki. 

Kwatsam sai ga jaruma Mansura Isah ta yi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram,mai cike da tonon silili, wacce ta harzukar da wasu daga jaruman fim din.


Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN