Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wani saurayi dan shekara 24 mai suna Habibu Sale bisa zargin kashe wata yarinya yar shekara 8 bayan ya saceta ya yi garkuwa da ita kuma ya karbi kudin fansa har N500,000 daga iyayenta.
Kakakin hukumar yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar cewa yansanda sun kama wanda ake zargin ranar Talata 17 ga watan Nuwamba. Ya ce Sale ya sace yarinyar mai suna Asiya Tasiu a kauyen Chikawa, da ke karamar hukumar Gabasawa ranar 6 ga watan Yuni 2020, lokacin da aka aiketa gidan Antinta da ke makwabtaka da gidansu.
An samo cewa ya bukaci a bashi N10m da farko, amma bayan tattaunawa ta fahimta, an ba shi N500,000.
DSP Haruna ya ce yan sanda sun yi nassarar kama Sale ranar 7 ga watann Nuwamba bayan sun bi diddiginsa daga jihohin Jigawa, Katsina, Kaduna, Abia da Kano inda aka cafke shi yayin da yake zaune a kofar gidansu.
Binciken yansanda ya nuna cewa Habibu ya kashe yarinyar ne saboda ya san za ta gane shi, kuma za ta tona masa asiri idan ya sake ta, saboda suna makwabtaka. Sakamakon haka ya kashe ta ya bizine gawarta a gefen kauyen Chikawa.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari