Sata ne aka yi mani a zabe, kuma wadanda suka yi wannan satan barayi ne>>Inji Donald Trump


Shugaban Amurka Donald Trump, ranar Lahadi, ya ce abin da ya faru a zaben shugaban kasar Amurka sata ne aka yi masa, kuma wadanda suka yi wannan satar barayi ne.

Trump ya sha kaye a hannun Joe Biden lokacin da ya sami kuri'ar Electoral College guda 279 daga adadin 270 da ake bukata dan takara ya kawo, kuma wanda ya fara kawo adadin kuri'un shi ne ya lashe zabe.

Trump wanda yake cikin fushi tun da Joe Biden dan takarar jam'iyar Democrat ya fara bayar da tazara mai yawa a kuri'u, ya yi ta nanata cewa an tafka magudi a zaben da aka yi domin a baiwa Joe Biden nassara, amma ya kasa kawo kwararan hujjoji.

Trump cikin bacin rai ya ruwaito a shafinsa na Twitter cewa "Mun yi amanna cewa wadannan mutane barayi ne. Gurbatattun mutane ne kawai. An tafka sata ne kawai a wannan zabe".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN