• Labaran yau


  Rundunar yansandan Najeriya ta karyata labarin karin albashin jami'anta


  Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ƙaryata labarin da ake yaɗa wa game da ƙarin albashin jami'anta.

  An ta yaɗa jerin tsarin albashin jami'an ƴan sanda a kafofin sada zumunta na intanet, inda a ciki aka bayyana cewa ƙaramin jami'in ɗan sanda konstabul zai karbi N84,000, yayin da kuma albashin kwamishinan ƴan sanda zai kai naira miliyan ɗaya da rabi.

  Amma rundunar ƴan sandan ta ƙaryata labarin inda ta wallafa takardar da ke ƙunshe da jerin tsarin albashin a shafinta na Twitter tare da tambarin labarin ƙarya.

  Rundunar ta kuma buƙaci ƴan Najeriya su yi watsi da labarin wanda dinga yaɗa wa. 

  Source: BBC


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rundunar yansandan Najeriya ta karyata labarin karin albashin jami'anta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama