Rayuwa: Me ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya daina saka Kufta?


Ɗabi’ar kwaikwayar yadda shugabanni ke sanya sutura ba sabon abu bane Najeriya. Domin tun daga salon saka jar hula ta marigayi Malam Aminu Kano da samfurin saka hula babu kari (Karyawa) ta tsohon shugaban ƙasa marigayi Shehu Usman Aliyu Shagari, har zuwa adon falmaran na marigayi tsohon gwamnan jihar Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, da kuma salon saka hular gashi na marigayi Sabo Aliyu Bakin Zuwo.

Haka ma ƴan Najeriya sun kwaikwayi yadda tsohon shugaban ƙasa marigayi janar Sani Abacha ya ke sanya riga samfurin Tazarce. Hakazalika ƴan Najeriya sun kwaikwayi yadda tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ke sanya hula samfurin Malafa.

Soyayyar Shugaba Muhammadu Buhari A Gurin Ƴan Najeriya

Tauraruwar shugaba Muhammadu Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka bashi mukamin ministan man fetur da ma’adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin sojin Janar Olusegun Obasanjo.

Haka kuma kasancewar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kudaden rarar man da kasar nan ta samu a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, domin gudanar da ayyukan ci gaban al’umma, ya ƙara sanya ƙaunarsa a tsakankanin talakwa Najeriya.

Hakazalika ayyukan da Janar Buhari ya yi wa Najeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu ya sa wasu ‘yan Najeriya ke son ganin ya sake zama shugaban kasar nan.

Shugaba Buhari Da Salon Adon Suturar Kufta

Bayan ɗarewar shugaba Muhammadu Buhari mulkin Najeriya a shekarar 2015, inda ya kayar da shugaba mai ci wato Goodluck Ebele Jonathan, ya zo da salon sanya sutura irin na tsofaffin ƴan bokon arewacin Najeriya da su ka samu kan su a ƙasar Burtaniya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zo karagar mulkin Najeriya da ɗabi’ar sanya Kufta tare da farar riga daga ciki.

Tasirin ƙauna da soyayyar da ake yiwa shugaba Muhammadu Buhari ya sanya al’umma (ma’aikata da ƴan siyasa) musamman a yankin arewacin Najeriya, su ka fara kwaikwayon yadda Buharin ya ke sanya sutura, har ake kiran abin da Buhari Style.

Shugaba Muhammad Buhari ya ɗauki tsahon lokaci yana irin wannan shiga ta Kufta, domin a ƙalla ya ɗauki shekaru 3 yana irin wannan adon.

Yaushe Shugaba Muhammad Buhari Ya Daina Adon Kufta?

A ƙarshen mulkin shugaba Muhammadu Buhari na zangon farko aka daina ganin shugaban da kufta, haka kuma yana dawowa zangon mulki na biyu ya watsar da ɗabi’ar saka kuftar gaba ɗaya.

Haka kuma al’ummar da su ke kwaikwayon shugaban wajen saka tufafin Kufta samfurin Buhari Style, su ma a hankali su ka dinga watsarwa.

Me Ya Sa Shugaba Muhammadu Buhari Ya Watsar Da Adon Kufta?

Al’umma sun yi mamakin yadda a hankali shugaba Muhammad Buhari ya koma sanya tufafi samfurin Shadda da kuma farin yadi. Mun tuntuɓi wasu daga cikin ƴan Najeriya game da abin da su ke kallon ya sanya Buharin daina saka kufta.
Malam Ali Sabo jami’in yaɗa labarai ne a Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD da ke jihar Kano, ya bayyana cewa “Abin da ya ke faruwa shi ne, al’umma ya kamata su fahimta shi mulki wani abubne da ya ke chanja mutum daga dabi’arsa ta ainihi zuwa wacce shi kansa bai san da ita ba, ita wannan dabi’a ita ce masana kimiyar dan Adam suke kira da “Hakikanin Mutum”.

“Mutane da yawa lokacin da suke cikin talakawa ko da su ba talakawan ba ne su kan yi ɗabi’u irin na talakawan domin su kwatantu da su saboda su amince musu ko kuma wani dalili wadda su kadai suka sani, wannan abu ya faru da manyan mutane da yawa wadanda in suka samu mulki sai su fito da ainihin halayyarsu”

“To ni ina gani wannan chanji dabi’u da ake gani ga shugaba mai ci wadda bama na kayan sawarsa ba yana nuna ainihinsa ne wadda shi kansa bai san dashi ba sai yanzu” In ji Malam Ali Sabo.

Haka ita ma Hauwa Shu’aibu Gaya, wacce ƴar jarida ce ta bayyana cewa “Eh to kamar yadda muka sani Kowane mutum yana da zaɓi da kuma ra’ayi na sa na daban kan kayan sawa da kuma launinsu

“Babu shakka wannan yayin shiga da yake a wancan lokacin ba mamaki ita ce tafi burge shi ko yafi jin dadin yin ta ko kuma yake ganin tafi masa kyau a jiki wanda har takai da sauran al’umma na kwaikwayon wannan shiga ta sa musamman matasa”

“To daina wannan shiga a nawa tunanin ba zai rasa nasaba da canjawar ra’ayi ba, wanda ba wani sabon abu bane mutum ya canja kalar tufafin da yafi so daga Shudi zuwa launin Fari ko makamantansu ko kuma ya canja yanayin ɗinki daga wani zuwa wani” In ji Hauwa Shu’aibu Gaya

Abubakar SD wanda ɗan jarida ne ya bayyana cewa “wannan shigar ta yanzu tafi ta da mutuntaka, domin ta da din da ya ke yi tana fito da ramarsa, amma yanzu tana kara masa kwarjini”

Wani malami a sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Bashir Bala, ya bayyana cewa “Ban da masaniyar me yasa yayi hakan. Watakila yana da lalurar jin sanyi ne, daga baya kuma sai ya warke ya daina sakawa”

Haka shi ma Aliyu Umar Aliyu ya bayyana cewa “sauyin matakin rayuwa da ya samu shi ya sa ya chanza kayan da yake sawa”

Hassan Hamza ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa “kawai ina ganin ba shi da ra’ayin yin irin wannan shigar ne a halin yanzu. Ko kuma za ta iya yiwuwa da ma ya tsara wa kansa a shekara kaza na mulkinsa ga irin shigar da zai riƙa yi, a shekaru kaza ga irin shigar da zai riƙa yi, har ya gama”

Tuni dai shugaba Muhammadu Buhari ya koma sanya tufafi samfurin shadda ko kuma Farin yadi, domin tun bayan dawowarsa zangon mulkin Najeriya a karo na biyu, da ƙyar idan an ganshi da kufta sau biyar.

Koma dai ya abin ya ke kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar saka duk irin suturar da ya ke da ra’ayi.

Source: labarai24Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN