Matsafa a jihar Ogun sun kashe wata daliba tare da cinye namanta


Wata kotu a jihar Osun ta tsare wata mata da ɗanta da kuma bokansu bisa zargin su da kashe wata ɗalibar Jami’ar Jihar Legas, LASU, ‘yar aji huɗu, Favour Daley Oladele, tare da cinye namanta.

Waɗanda aka tsare ɗin su ne Bola Adeeko, da ɗanta, Owolabi Adeeko da bokansu, Segun Philip, kamar yadda jaridar Intanet, SaharaReporters ta rawaito.

Kemi Bello, jami’in da ya gabatar da ƙara daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Osun, ya maka mutanen uku a kotun ne bisa zargin haɗa kai don aikata laifi da kuma kisan kai.

Sai dai ba a karanta wa waɗanda ake ƙara waɗannan zarge-zarge ba saboda ba su da lauya

Mai Shari’a Grace Onibokun, ta ɗaga sauraron ƙarar zuwa 3 ga Maris, 2021, don ci gaba da sauraro, kuma ta bada umarnin a tsare waɗanda ake ƙarar a gidan gyaran hali.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ce ta kama bokan tare da mahaifiyar da kuma ɗanta bisa zargin kashe Misis Oladele.

Biyo bayan kamun nasu, Mista Owolabi ya bada labarin yadda shi da mahaifiyarsa suka haɗa baki don kashe budurwarsa a wancan lokaci, suka cinye namanta ta a yayin wani cin abinci irin na tsafi don su yi kuɗi.

Ranar 8 ga Disamba, 2019 ne marigayiyar ta ɓata, amma binciken ‘yan sanda ya sa aka gano waɗanda ake zargi da kashe ta a wata coci da har yanzu ba a bayyana sunanta ba.

Source: Labarai23


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN