Matsalar Tsaro: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar


Gaisuwa tare da fatan alkhairi a gareka ya mai alfarma Sarkin Musulmi.

Kamar yanda kowa ya sani cewa sarautar Sarkin Musulmi sarauta ce da babu kamarta a duk faɗin wannan ƙasa tamu Najeriya, saboda mun sani cewa tun a lokacin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo dukkan sarakunan Musulunci suna karɓar umarni ne daga wannan fada ta mai alfarma Sarkin Musulmi, saboda martabarta, ƙimarta, matsayinta, darajarta da kuma girmanta. Sannan kuma mun san cewa haƙƙin ne na wannan fada akan ta kula da duk wani abu da ya shafi al’ummar Musulmai da ke faɗin wannan ƙasa ta mu Najeriya.

Ya mai alfarma Sarkin Musulmi, a yanzu kowa yasan cewa yankin Arewa ya shiga wani mawuyacin hali wanda a wasu shekaru baya bamu taɓa tunanin cewa zamu samu kanmu a ciki ba, wanda a yanzu babu abinda yake fitowa daga bakin mu a kullum sai “Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un” saboda kusan a kullum babu wasu rahotanni da suke fitowa daga Arewa face labarin garkuwa da mutane, kashe al’ummar musulmai, cin zarafin al’umma da sauran abubuwa wanda ko ban faɗa ba kowa ya san dasu.

Ya mai alfarma Sarkin Musulmi, tun ba yanzu ba ya kamata ka jajirce akan ƴan’uwanka musulmai, saboda mu a yanzu babu wani abu da muke buƙata wanda ya wuce jagoranci, kamar yanda Manzon Allah (S.A.W) yace “Babu wata al’ummar da zata cigaba ba tare da jagoranci ba”. Don haka mu mun yarda da kai a matsayin jagoran Musulunci da Musulmai da suke faɗin wannan ƙasa tamu Najeriya.

Ya mai alfarma Sarkin Musulmi, muna so muji sautin muryarka akan wannan mummunan hali na taɓarɓarewar tsari da ƴan’uwanka musulmai na yanki Arewa suke ciki, sannan kuma muna buƙatar gagarumar gudummawarka wajen yin kira ga gwamnati akan a ɗauki duk wani matakin daya dace domin dawo mana da daraja, ƙima da kuma martabar wannan yanki namu na Arewa, wanda mafi yawa musulmai ne ƴan’uwanka suke rayuwa a cikinsa.

Ya mai alfarma Sarkin Musulmi, duk ɗan Arewa a kullum hankalinsa a tashe yake musamman idan aka ce wata tafiya ta kama shi zuwa wani waje daga cikin yankin na Arewa, saboda wannan mummunar ɗabi’a ta sace mutane ta zama abinda ya fi komai sauƙi a yanzu, wanda hakan shine ya jefe tsoro mai tsanani ga mu al’ummar wannan yanki na Arewa.

To ina fata zaka duba wannan wasika tawa da idanun basira ba tare da duba ƙanƙantar shekaruna ba, sannan kuma a ɗauki duk irin matakin daya kamata a ɗauka, domin kawo ƙarshen wannan matsala.

Daga karshe ina addu’ar Allah (S.W.T) Ya taimaki musulunci da musulmi ya kuma cigaba da ƙasƙantar da kafirci da kafirai.

Allah (S.W.T) ya kawo mana ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a wannan yanki namu na Arewa da ma ƙasar mu baki ɗaya.

Source: labarai24


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN