NSCDC za ta hukunta jami'anta da suka yi wa VIO duka a kan hanyar Abuja zuwa Keffi


Shugaban jami'an tsaron farin kaya na NSCDC na Najeriya Mr. Abdullahi Gana, ya yi allah wadai da matakin famakin jami'an VIO da wasu daga cikin jami'an NSCDC suka yi a kan hanyar Abuja zuwa Keffi.

Jami'an VIO na gudanar da akin kula da ababen hawa a kan hanyar lokacin da jami'an NSCDC suka isa wajen cikin wata babban Bas da ke dauke da jami'an kan hanyarsu ta komawa gida. Rahotanni sun ce an sami yar damuwa tsakanin jami'an VIO da na NSCDC wanda ya kai ga jami'an NSCDC suka ci zarafin jami'an VIO.

NAN ta labarta cewa Kakakin NSCDC na kasa Mr Kalu Okeh, ya ce hukumar NSCDC za ta hukunta jami'anta da ke da hannu a wannan aika aika. 

Ya kuma ce hukumar ta jaye motar Bas da ke daukan jami'anta zuwa Keffi wajen zuwa da komawa gida idan an tashi daga ofis sakamakon wannan matsala


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN