Asibitin koyarwa ta LAUTECH ta kwace gawan saurayi sakamakon rashin biyan kudin Asibiti


Ana zargin hukumar Asibitin koyarwa na Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Osogba ta kwace gawar wani saurayi dan shekara 20 mai suna Ayomide Taiwo wanda ya mutu ranar 9 ga watan Agusta 2020 kwanaki kadan bayan wani safeton yansanda  mai suna Ago Eghareyba wanda ke aiki a ofishin yansanda na Obokun ya doke shi a kai da gindin bindiga saboda ya ki ya bashi na goro N50.

Iyayen mamacin ne suka shaida wa manema labarai cewa hukumar gudanarwa na Asibitin ta kwace gawar yaron ne saboda ragowar kudin Asibiti da ba a biya ba.

Ayomide ya gamu da ajalinsa ne a hannun safeton yansanda a wajen shingen bincike na yansanda a karamar hukumar Iragbiji Boripe na jihar Osun ranar 3 ga watan Agusta, yayin da yake dawowa daga garin Owena a jihar Ondo bayan ya yi shagulgulan Sallar Layya tare da Mahaifiyarsa bayan rasuwar Mahaifinsa.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN