Wani mutum ya kuwata yayin da ake yi masa bulala 150 a garin Idi da ke gundumar Aceh na kasar Indonesia ranar Alhamis sakamakon kama shi da laifi da Kotu ta yi na yin lalata da karamar yarinya, bisa wannan dalili aka yi masa hukunci.
Rahotanni sun ce mutumin ya kuwata tare da kuka a laokacin da ake yi masa bulala da icen rattan, ya kuma bukaci a dakata. Likitoci sun duba shi kafin daga bisani aka karkare bulalan guda 150 .
Gundumar Aceh na bin dokokin Islama sau da kafa, kuma tana zartar da hukunci ga masu laifi bisa tsarin dokokin addinin Islama.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari