• Labaran yau


  EndSars: An kama mutum 2 da suka ci gasashshen naman yansanda da aka kashe a Oyo


  Rundunar 'yan sanda reshen jihar Oyo, ta tabbatar da kama mutum biyu kan zarginsu da cin gasashen naman 'yan sandan da aka ƙona yayin zanga-zangar EndSars.

  BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Oyo, Fadeyi Olubenga, inda ya tabbatar da cewa an tasa ƙeyar mutum biyun a yau Asabar a Ibadan babban birnin jihar.

  Ya ce an ƙaddamar da binciken neman waɗanda suka yi wannan aika-aikar ne bayan wani bidiyo da aka rinƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane suka kashe 'yan sanda da ƙona su, da amfani da adda suna daddatsa naman su suna ci.

  Ya kuma bayyana cewa an tafi da waɗanda ake zargin zuwa hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike.

  Source: BBC


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: EndSars: An kama mutum 2 da suka ci gasashshen naman yansanda da aka kashe a Oyo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama