Matasa sun aika wani matashi barzahu da gaggawa suka kone gawarsa, duba dalili (Hotuna)


Fusatattun matasa sun banka ma wani da ake zargi barawo ne wuta bayan sun kashe shi a garin Idjerhe da ke karamar hukumar Ethiope ta kudu a jihar Delta ranar Talata 24 ga watan Nuwamba.

ISYAKU.COM ya samo cewa wanda aka kama yana daya daga cikin gungu 2 na masu aikatab laifi da ke addabar mutane a yankin. Ya bi wata yarinya ya razanata da bindigar roba ya karbe waya da kudade da ke hannunta.


Rahotanni sun ce bayan yarinyar ta kula cewa bindigar roba ne, sai ta yi kururuwa har matasa suka nufo wajen, sakamakon haka barawon ya ruga da gudu kuma jama'a suka biyo shi har suka kama shi suka yi masa duka har ya mutu, daga bisani suka banka wa gawarsa wuta.


Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar da aukuwan lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN