2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai

Akasin kiran da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yayi na batun karba-karba tsakanin yankunan Najeriya wurin mulki, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce karba-karba ba zai taimaki Najeriya ba, ko kuma kawo karshen matsalolin da kasar nan take fuskanta ba.

Premium Times ta ruwaito yadda gwamnan yayi wannan jawabin a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, yayin da yake jawabi a kan yadda 'yan Najeriya daga kowanne yanki suke kwadayin mulki, a taron NES.

El-Rufai ya ce batun karba-karba ba zai taimaki kasa ba.

Legit.ng ta tattara bayanai a kan yadda batun shugabanci karba-karba tsakanin arewa da kudu ya zama al'ada tun da aka fara siyasa a 1999.

El-Rufai ya ce cancanta ya kamata a yi amfani dashi wurin zaben shugaban kasar Najeriya.


A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari yankin Yolde pete da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Mazauna yankin tare da jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, miyagun dauke da makamai sun tsinkayi gidan dansanda makusancin Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, an gano cewa 'yan bindigan sun so tarar da dan sandan ne bayan sun zargi sun iso gari tare da Atiku Abubakar.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari