An ceto 'yammatan Katsina 26 daga hannun 'yan bindigar Zamfara


Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce kwalliya tana biyan kuɗin sabulu a tattaunawar sulhun da ake yi da ƴanbindiga daɗi a jihar, sakamakon sakin ƴanmata 26 ƴan asalin jihar Katsina wanda dukkan su yara matane masu ƙarancin shekaru.

An saki ƴanmatan ga gwamnatin jihar Zamfara ba tare da biyan kuɗin fansa ba, a cewar mai magana da yawun gwamna, Zailani Baffa. Sai cikin sa'a gwamnatin Zamfara ta samu nasarar ganosu tare da ceto su ta hanyar haɗinguiwa da ƴan bindigar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran.

Kwamishinan ne ya wakilci gwamna Matawalle a tattaunawar sulhu da ƴan bindigar a ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya a jihar. Gwamna Matawalle, wanda ya karɓi kuɓutattun ƴan matan, ya ce gwamnatinsa ba zata yi watsi da tattaunawa don wanzar da zaman lafiya ba. Ya ƙara da cewa amfani da ƙarfin bindiga kaɗai ba shi zai kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga ba a jihar.

Ya ce "wannan shine mahangar mu ta yin sulhu da ƴan bindigar a tattaunawar sulhu don wanzuwar zaman lafiya a jihar Zamfara. "Waɗanda suka yarda cewa bamu yi dai-dai ba da muka yi sulhu da ƴan bindigar, basu san cewa kuɓutar da ƴanmatan, ba karamar nasara ce marar misaltuwa ba".

"Ƴammatan 26 da aka ceto, wanda shekarunsu ke tsakanin 8 zuwa 12, an duba tare da tantance lafiyarsu kuma an basu sabbin kayan sawa," a cewar Matawalle. Gwamnan ya bayar daumarnin a mayar da ƴammatan jihar Katsina. Ceto ƴanmatan ya kara adadin ƴammata da mutanen da aka ceto zuwa sama da arba'in daga makon da ya gabata.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN