Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka


An haifi Jospeh Biden Jr ne a ranar 20 ga watan Nuwamban 1942. Biden dan siyasar Amurka ne kuma zababben shugaban Amurka bayan ya yi nasara kan Shugaba Donald Trump a zaben shugaan kasa na 2020. Za a rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 46 a watan Janairun 2021.

 Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ka sani game da shi kamar yadda The Nation ta tattara.

1. Biden dan jam'iyyar Democratic Party ne, a baya ya rike mukamin mataimakin shugaban Amurka na 47 daga 2009 zuwa 2017 sannnan ya rike mukamin sanata mai wakiltar Delaware daga 1973 zuwa 2009.

2. Ya girma ne a Scranton, Pennsylvania da New Castle County a Jihar Delaware.

3. Biden ya yi karatu a Jami'ar Delaware kafin daga bisani ya yi karatun digiri daga Jami'ar Syracuse a shekarar 1968.

4. An zabe shi kansila na New Castle a 1970 ya kuma zama sanata mafi karancin shekaru na shida a tarihin Amurka a lokacin da aka zabe shi sanatan Amurka daga Delaware a 1972.

5. An zabi Biden a matsayin sanata har sau shida kuma shine sanata na hudu cikin wadanda suka fi yawan shekaru a majalisar a lokacin da ya yi murabus don ya zama mataimakin Shugaba Barack Obama.

6. A watan Afrilun 2019, Biden ya sanar da cewa zai yi takara kuma ya samu kuri'un wakilai da ya bashi damar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democratic Party a Yunin 2020.

7. Biden na mataimakin shugaban kasa na biyu a tarihin Amurka da ya zama zababben shugaban kasa bayan ya sauka daga mulki tun bayan Richard Nixon a shekarar 1968.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN