Muna samun N5,000 daga kwanciya da maza 5 zuwa 7 - Karuwai


Wata mata mai suna Etiennette Ajoluje, ta bayyana abubuwan da ta gano da tayi cudanya da wasu karuwai a wata anguwa da ke jihar Legas, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Bayan ta kai wa gidan karuwan ziyara a ranar Juma'a, 6 ga watan nuwamba, ta gano cewa karuwa guda daya tana iya samun a kalla N5000 kullum idan ta kwanta da maza 5 zuwa 7. Ta gano kusan karuwai 4 da ke dauke da juna biyu, sai wata wacce take goyon jariri mai watanni 16 da haihuwa.

Kamar yadda Ajoluje ta bayyana, karuwan da ta tattauna da, sun tabbatar mata da cewa a shirye suke su bar karuwanci. Kamar yadda ta wallafa: "Suna samun N5000 idan sun kwanta da a kalla maza 5 zuwa 7 a rana. "Watanni 3 da suka gabata, wata kyakkyawar yarinya ta same ni da hawaye share-share, tana rokona in taimaka mata ta bar rayuwar bariki.

"Karuwa ce, ta kirani kwanaki 4 da suka wuce, shiyasa nayi wannan wallafar. Na kai ta wani wurin cin abinci (Mama put) inda muka ci, muka sha. Sai da na tabbatar hankalinta ya kwanta, tukunna na tambayeta matsalarta.

"Tana kwanciya da a kalla maza 5 zuwa 7 a rana, kowannensu yana bata N500 zuwa N1000. Ta kaini gidan karuwan da take biyan N1000 kullum."Na hadu da wata mata mai jariri dan shekara daya da watanni 4 da haihuwa a wannan gidan karuwan.

Goma daga cikinsu cikin hawaye sun tabbatar min cewa suna so su tuba. Akwai masu gyaran gashi, teloli, masu girke-girke da sauransu a cikinsu. Ku taimaka jama'a.

Ku bani shawara a kan wannan al'amarin. Ni 'yar sako ce. A wani labari na daban, 'yan kwamiti sun ki amincewa da kasafin shuguban INEC, gidan talabijin na Channels suka nuna hakan a ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.

A ranar Laraba ne kowa ya gabatar da kasafi ga 'yan majalisar wakilai, inda wasu 'yan kwamitinsa suka ki amincewa da kasafin da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar a kan ayyukan 2020. Majalisar dattawa sun bukaci zantawar sirri tsakanin su da shugaban INEC din ba tare da tawagarsa ba, dangane da kasafin.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN