Dan dagacin kauye ya mutu bayan arangamar jami'an kwastam da 'yan sumogal


Dan dagacin wani kauye ya rasa ransa sakamakon rikicin jami'an kwastam da wasu matasa 'yan sumogal a jihar Kebbi., jaridar The Punch ta wallafa.

Rikicin ya hargitse tsakanin jami'an kwastam na Kaduna da suke aiki a jihar Kebbi, da wasu matasa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi.

Kamar yadda rahotonni suka kammala, wanda aka kashe, Abdul-Rahman Sani, da ne ga dagacin kauyen Budi, Alhaji Sani Muhammad, na karamar hukumar Bunza.

Tsohon sakataren kungiyar bunkasa karamar hukumar Bunza, Alhaji Sahabi Chindo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, "Jami'an kwastam sun tare wasu ababen hawan matasan garin Bunza.

"Matasan sun tsaya suna ciniki da jami'an, bayan sun gama, sai matasan suka je daukar ababen hawansu, kawai sai rikici ya hada jami'an da marigayin.

"Jami'an sun dakatar da Abdul-Rahman, inda suka ce in dai ya matsa kusa da su za su harbeshi, yana matsawa suka harbeshi."

Kakakin hukumar kwastam na Zone B, na Kaduna, ASP Mailafiya Magaji, yace, "Yayin da jami'ansu suna sintiri wuraren layin Kamba kusa da Bunza, sai suka ci karo da wani abin hawa cike da shinkafa 'yar kasar waje, wacce nake kyautata zaton sumogal din ta aka yi."

A cewar Magaji, "Bayan jami'an sun ci karo da matasan, kawai sai ga wasu matasan daban, dauke da makamai. Hakan ya janyo rikici tsakaninsu.

"Matasan sun yi yunkurin kai wa jami'an farmaki, sai suka yi harbi, inda alburushin ya sami daya daga cikin matasan a kafadarsa ta hagu, take a nan aka kai shi asibiti.

"Duk da dai wasu daga cikin jami'an sun samu raunuka, amma matashin ya rasa ransa babu dadewa da kai shi asibiti."

A wani labari na daban, Murtala Gwarmai, mai ba wa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin matasa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya rarraba wa matasa jakuna a ranar Alhamis.

Gwarmai, ya gwangwaje matasan da jakuna, babura da kekunan hawa da sauran su, Daily Trust ta wallafa. Kamar yadda rahotonni suka kammala, matasa a kalla 40 ne suka sha daga romon damokaradiyyar.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN