Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga


Fadar Shugaban kasa ta ce duk wadanda suka bari zanga zangar #EndSARS da aka yi kwanan nan ya zama rikici da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi a kasar sai sun biya bashin abunda suka aikata.

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayinda ya bayyana a shirin Channels TV.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya ta daskarar da asusun mutane 20 da suka jagoranci zanga zangar #EndSARS yayinda aka hana wata da ta daukaka gangamin, Modupe Odele, fita kasar waje a makon da ya gabata.

Har ila yau hukumar kula da shige da fice ta kwace fasfot dinta.

Da aka tambaye shi ko ubangidansa na sane da ci gaban, Shehu ya ce lamarin ya isa teburin Shugaban kasar, inda ya bayyana cewa dole masu zanga zangar su fuskanci doka.

Ya ce: “Kasar nan shugaba daya ne da ita sannan kundin tsarin mulki daya ne da ita. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke rike da gwamnati. Lamarin ya sauka a teburinsa.

“Mun kasance kasa da ke jagoranci da doka. Akwai kundin tsarin mulki – karkashin sashi na 33 – cewa karara ya baiwa al’umma yancin yin zanga zangar lumana amma idan zanga zangar lumana ya zama rikici, da sace sace, akwai bukatar ayi aiki da doka da oda.

“Kowa ya ga tarin sace sace da aka yin a kayayyakin gwamnati da masu zaman kansu musamman a Lagas, Calabar, Filato, Taraba da wasu jihohi, harma da babbar birnin tarayya.

“A yanzu, ya zama dole a bari dokar kasa ta yanke hukunci, ta yi hukunci kan barnar da aka yi ta bangaren kowanene.

“Ba wai ina magana musamman a kan fitattu ko wadanda suka daukaka ta ba amma dai an yiwa kasar nan ba daidai ba kuma dole mutane su shirya girbe abunda suka shuka.”

Ya kara da cewa wasu yan siyasa, wadanda suka daukaka zanga zangar #EndSARS ciki harda na PDP “su fito su yi Allah-wadai da barnar da zanga zangar ya haddasa a bainar jama’a.”

A gefe guda, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi zargin cewa masu daukaka zanga zangar EndSARS na so su yi amfani da shi ne wajen sauya gwamnati.

Dan majalisar a yayin wata hira da jaridar Daily Trust, ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan Najeriya ne ke daukar nauyin zanga zangar EndSARS domin kaskantar da arewa.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN