Buhari: Ba zai yuwu mu cigaba da tsame matasa ba wurin yanke hukunci


Shugaba Buhari ya ce rikicin EndSARS alama ce ta fusatar matasan Najeriya.

A watan Oktoba, 'yan Najeriya da dama sun yi ta zanga-zanga a tituna suna bukatar a gyara lamarin 'yan sanda. The Cable ta wallafa.

Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Gambari ya roki gwamnonin kudu maso yamma da su yi gaggawar gyara al'amarin tun daga tushe.

Shugaban kasar ya ce ba maganar fatar baki ya kamata shugabanni su tsaya yi ba, ya kamata su samar wa da matasa ayyukan hannu.

A cewarsa "Da idanunmu mun ga yadda zanga-zangar lumana ta koma hargitsi da tashin hankali, wanda hakan ya rikitar da dukkaninmu.

"Abinda muka gani alama ce da ke nuna ya kamata mu yi hobbasa mu kawo gyara. Wajibi ne mu tabbatar mun samar da zaman lafiya duk tsanani duk rintsi."

Ooni ya ce zai samar da wata gaba, wacce za ta hada shugabannin gargajiya wuri guda idan matsala irin wannan ta taso, don a yi gaggawar dakatar da ita.

A wani labari na daban, jaridar Leadership ta wallafa cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya wadanda har ya zuwa yanzun basu lashi romon gwamnatinsa ba, da kuma wadanda su ke ganin gazawar gwamnatin, da su yi hakuri.

Ya yi wannan roko a ranar Juma'a a garin Ilorin a wurin taron fadi-ra'ayinka. Taron wanda an yi shi ne saboda zanga-zangar EndSARS da kuma sakamakon da ta haifar.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN