• Labaran yau


  Hotunan yadda Ganduje tare da Hisbah suka kone kwalaben giya na N200m a Kano


  Hukumar Hisbah na jihar Kano ta kone kwalabe Miliyan daya da dubu dari tara da saba'in da biyar (1,975,000) na kimanin kudi Naira Miliyan dari biyu. N200m.

  An gudanar da kone kwalaben giyar ne ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba a Kalebawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa karkashin jagorancin Gwamna Umar Ganduje.


  Yayin da yake jawabi a wajen kone kwalaben, Gwamna Ganduje, wanada mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya ce, shan barasa tare da wasu ababen da ke sa maye kuma ke gusar da hankalin dan Adam, Musulunci ya haramta mu'amala da su.


  Rahotun Isyaku Garba


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan yadda Ganduje tare da Hisbah suka kone kwalaben giya na N200m a Kano Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama