Jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun yi nassarar ciro wani yaro dan shekara 6 da ya fada a cikin wata rijiya mai zurfi a Yansango da ke karamar hukumar Kumbotso.
Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Laraba 4 ga Satan Satumba.