Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya karbi manyan yan bindiga biyu da suka tuba a gidan Gwamnatin jihar Katsina. Sale Turwa da Muhammed Sani Maidaji sun tuba kuma suka mika makamansu ga Gwamnati.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Kwamishinan yansandan jihar Katsina Aminu Baba da takwarorinsa na Briged na 17 na soji da ke Katsina, Daraktan DSS da Kwamandan NSCDC na jihar Katsina ne suka gabatar wa Gwamna Masari da tubabbun yan bindigan da suka dade suna addaban jihar.
Kwamishinan yansandan jihar Katsina ya ce manyan jami'an tsaron jihar sun bukaci Gwamna Masarai ya duba nadama da tuba da yan bindigan suka yi kuma ya yafe masu domin su zama mutane na gari a cikin al'umma.
Ya ce wannan babban nasara ce wajen yaki da yan bindiga kuma Gwamnati a shirye take domin yafe wa tubabbun yan bindiga da suka gabatar da kansu.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari