• Labaran yau

  Gwamna Bello Matawalle ya ceto mutum 11 daga masu satar mutane ba tare da biyan fansa ba


  An ceto mutum 11 daga hannun masu sace mutane domin karban kudin fansa a jihar Zamfara tare da taimakon Gwamnan jihar Zamfara.

  Rahotanni sun ce Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ne ya yi sanadin kubutar mutanen kuma ba tare da biyan kudin fansa ba.


  Sakataren watsa labarai na Gwamnatin jihar Zamfara Jamilu Iliyasu Magaji ne ya sanar da haka ranar Lahadi da dare.  Ya ce wannan ya samu ne sakamakon wani shirin Gwamnati na "Karas ko icce". Ya ce Gwamnati za ta yi duk abin da za ta iya yi domin bayar da tsaro ga al'umman jihar Zamfara.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamna Bello Matawalle ya ceto mutum 11 daga masu satar mutane ba tare da biyan fansa ba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama