Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin kama Rahama Sadau


Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta bayar da umarnin kamawa da bincikar fitacciyar 'yar fim ɗin nan Rahama Sadau, bayan wani ya kai ƙarar ta ga 'yan sandan kan wasu hotuna da ta wallafa da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Sai dai a bayanan da BBC ta samu, 'yan sandan ba su samu nasarar kama Rahamar ba saɓannin yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, amma majiya mai ƙarfi ta nuna cewa tana ƙoƙarin haɗa tawagar lauyoyinta da za ta je da su ofishin 'yan sandan domin kai kanta.

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ne ya bayar da umarnin kamar Rahamar bayan wani mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam mai suna Alhaji Lawal Mohammed Gusau ya aika wa babban sufeton da wasiƙa bisa cewa Rahamar ta aikata saɓo ga annabi.

A takardar koken da Alhaji Lawal ya aika wa babban sufeton, ya shaida wa babban sufeton cewa abin da Rahama ta aikata zai iya jawo rikici domin kuwa tuni wasu malamai da matasa suka fara barazanar É—aukar mataki, a cewarsa.

Ya kuma yi wa babban sufeton matashiya kan abin da ya faru a Kano a 'yan kwanakin nan da kuma a Faransa wanda ya ce dama tuni al'ummar Musulmi abin ya kai su bango.

Ya kuma buƙaci babban sufeton ya yi la'akari da cewa bai kamata Najeriya ta ƙara tsunduma cikin wani rikici ba a daidai lokacin da take ƙoƙarin farfaɗowa daga tarzomar da ENDSARS ta jawo.

Da alama babban sufeton ya samu wannan wasiƙa ta Alhaji Lawal cikin hanzari, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya bayar da umarni ga kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kaduna domin gaggauta ɗaukar mataki don tabbatar da cewa wannan lamari bai haifar da wani abu na rashin tsaro da tada hankalin jama'a ba, kamar yadda takardar da Babban Jami'in Ofishin Sufeto-Janar mai suna DCP Idowu Owohunwa ya rattaɓa wa hannu ta nuna.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Lawal Gusau, wanda ya kai Rahama ƙara domin jin ƙarin bayani, amma bai ɗaga waya baya.

Sai dai Mujallar Fim ta ruwaito cewa Alhaji Lawal Gusau ɗin sananne ne wajen shiga al'amuran da suka shafi harkar fina- finan Hausa, domin kuwa, ko a kwanakin baya sai da ya kai ƙara a kan bidiyon tsiraici wanda ake zargi na Maryam Booth ne da aka yi ta yaɗa shi a kafafen sada zumunta a kwanakin baya.

A cikin makon nan ne dai Rahama Sadau ɗin ta wallafa wasu hotuna waɗanda suka nuna surar jikinta, wanda hakan ya jawo wani ya yi maganar ɓatanci game da Manzon Allah (SAW) a ƙasan hotunanta da ta saka.

Sai dai daga baya jarumar ta fito ta ce sam ba da yawunta aka yi waɗannan kalaman ɓatancin ba, inda har ta yi bidiyo tana kuka tana roƙon gafarar Musulmai da waɗanda abin ya ɓata wa rai.

Tun kafin ta nemi gafarar, abokan sana'arta da dama na Kannywood sun fito sun yi mata raddi mai zafi, haka ma wasu sanannun mutane a kafafen sada zumuntar sun yi mata raddi da jan kunnenta.

Sai dai bayan haƙurin da ta bayar da kuma nadamar da ta yi, wasu sun sassauta kalamansu kanta da ba ta shawarar kada hakan ya sake faruwa, wasu kuma na nan a kan bakarsu na cewa ba za su yafe mata ba.

Source: BBC


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN