Ba za mu aminta da nassararka ba, kotu ce za ta warware magudi da aka yi - Lauyan Trump


Duk da yake kafofin watsa labarai da dama sun labarata cewa Joe Biden dan takaran shugaban kasa a jam'iyar Democrat ne ya lashe zaben da aka gudanar na shugaban kasar Amurka, Rudy Giuliani, tsohon Magajin garin New York kuma Lauyan dan takaran jam'iyar Republican, kuma shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce har yanzu da sauran rina a kaba domin ya ce an tafka gagarumar magudi, kuma Kotu ce kawai za ta warware wannan badaakala.

Bangaren shugaba Trump sun gabatar da zargin magudi a wasu jihohi, sun ce da yiwuwar Trump zai yi nassara a wadannan jihohi daga Biden.

Sun ce ranar zabe 3 ga watan Nuwamba, Trum na jagorantar nassara da yawan kuri'u a jihohi da ake wa kallon fagen daga azaben. Sun yi zargin cewa daga bisani nassarar  Tump  ya fara ja da baya bayan kuri'u da aika aika ta hanyar wasiku suka fara ba Biden jagoranci wanda ya nuna cewa da dawalaki cikin wannan tsarin.

Bayan an sanar da nassarar Biden a amatsayin wandaya lashe zaben shugaban kasar Amurka ranar 7 ga watan Nuwamba, Trump ya fitar da sanarwar cewa "Mun san dalili da ya sa  Joe Biden yana hanzarin nuna cewa shi ne ya yi nassara a zabe, kuma da dalili da ya sa kafofin labarai da ke goyon bayansa aiki tukuru domin taimakonsa. Basu son su fadi gaskiya, amma har yanzu wannan zabe bai kammalu ba" inji Trump.

A wani jawabi da Rudy Guiliani ya yi a wajen taro a Philadelphia, ya ce "Trump ba zai aminta da sakamakon zaben ba yayin da har yanzu akwai kuri'u 600,000 da ba a tabbatar da makomarsu ba lokacin da aka dakatar da zabe kuma aka sanar cewa Biden ne ya yi nassara", kamar yadda ya yi zargi.

Kazalika Guiliani ya yi zargin cewa ba a bari masu sa ido a zaben na Republican suka matsa kusa kwarai domin su gani ko kuri'u da ake kadawa ingantattune ba ko akasin haka.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN