Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa


Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda tauraronsa ke kan haskawa a masana’antar shirya fina-finan ta Hausa, Nuhu Abdullahi na shirin angwancewa. Za a daura auren Nuhu tare da amaryarsa Jamila Abdulnasir a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, a jihar Kano.Tuni dai manyan jaruman masana’antar da shi kansa angon suka fara wallafe-wallafen hotunan kafin auren masoyan biyu. A hotunankafin auren nasu wanda Legit.ng ta gano a shafin jarumin na nuhuabdullahi a Instagram, an gano masoyan biyu sanye da kayayyaki na alfarma da kamala.A cikin daya daga cikin hotunan, amaryar ta kasance sanye da atamfa launin ruwan kasa da launin ruwan gwal yayinda shi kuma angon ya saka dinkin babbar riga launin ruwan kasa shima. A wani hoton kuma, angon ya saka farin shadda dinkin babban riga inda ita kuma sahibar tasa ta sanya dinkin doguwar riga launin ruwan hoda. Sun kuma rike junansu a hoton cike da shauki.Jarumin ya kara shahara sakamakon wani shiri mai suna Labarina da masana’antar ke haskawa a yanzu wanda ya dauki hankalin ma’abota kallon fina-finan Hausa.

Source: legitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN