Yan Najeriya sun biya wa matar da asibiti ta tsare wata 7 bayan haihuwa cikon kudin aiki


Wasu yan Najeriya sun biya cikon kudin da Mojol Hospital ke bin Blessing Bassey, mata da ta haihu a Asibitin kuma ta kasa cika N95,000 da Asibitin ke binta daga cikin  N250,000 da aka yi mata aikin fitar da Jariri wajen haihuw, a unguwar Choci da ke Shasha a birnin Lagos.

Bayan da Jaridar Punch ta ruwaito labarin ne a ranar 2 ga watan Oktoba 2020, mutane da dama a fadin Najeriya sun bukaci su biya mata kudin.

Daga cikinsu har da kungiyoyi kamar Right and Welfare of Traumatised Wives da Youths Initiative, Global Medical Organisation, da kuma sauran kungiyoyi da jama'a da basu son a ambaci sunansu.

Blessing yar shekara 27, ta gode wa Jaridar Punch da ta wallafa labarin, wanda ya yi sanadin da jama'a suka kawo mata dauki. Ta ce " Ba domin wannan Jarida ba, da har yanzu ina kwanciya a doron simintin wannan Asibiti a kasa tare da Jaririna".

Idan baku manta ba, Mojol Hospita ta rike Blessing ne ta hana ta komawa gida wata bakwai bayan ta haihu a Asibitin, bisa dalilin cewa ta kasa cika N95,000 ragowan kudin aikin tiyata N250,000.

 

KALLIYADDA SABO SARKIN ZAZZAU YA SHIGA FADA LATSA NAN


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN